GETTY IMAGES
Wasu al'ummomi a jihar Zamfara ta Najeriya sun kaurace wa kasuwannin kauye saboda yadda wasu da ake kira 'yan sa-kai ke shiga suna kashe mutane da sunan farautar barayi da 'yan fashi.
Kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talatar Mafara na daya ga cikin babbar kasuwar kauye da ke ci duk Lahadi a zamfarar.
Fulani da mutanen kauyen da ke cin kasuwar sun ce 'yan sa-kai na shiga kasuwar su kama sannan su kashe mutanen da suke zargi suna da alaka da barayi
A tattaunawarsa da BBC, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce jami'ansu na taka muhimmiyar rawa wajen kawar da bata gari da kokarin inganta tsaro a kewayen kauyuka da birnin Jihar.
Sai dai ya ce la'akari da matsalolin tsaro da jihar ke fama da su kowa na da alhakin tuntubarsu ko bada gudunmawa wajen kawar da masu tada kayar baya.
SP Muhammad ya kuma umarci kowanne mutum ya kasance mai sa ido da ankarar da jami'an tsaro a duk lokacin da aka fuskanci wasu na kokarin tada zaune tsaye.
Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa a baya-bayan nan, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen ayyukansu.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.

Karin bayani game da Zamfara:
- Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
- Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
- Take: Noma tushen arzikinmu
- Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
- Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
- Musulmi ne mafi yawa
- Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
- Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu
Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara - Daga Kadariyya Ahmed
Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.
A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.
Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.
Source@bbchausa
No comments:
Post a Comment