Monday, December 17, 2018

Atiku ya taya Buhari murnar zagoyar ranar haihuwa

Shugaba Muhammadu Buhari yana bikin zagayowar ranar haihuwarsaHakkin mallakar hotoMBUHARI / TWITTER
Image captionShugaba Muhammadu Buhari yana bikin zagayowar ranar haihuwarsa
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaban na Najeriya ya cika shekara 76 da haihuwa ranar Litinin 17 ga watan Nuwambar bana.
A sakon da ya wallaf aa shafinsa na Tiwita, Atiku Abubakar ya ce yana taya shugaban kasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
"Ina taya Shugaba @MBuhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kuma ni da iyalina muna masa addu'ar tsawon rai
Ya kara da cewa: "Duk da cewa ni da shi za mu hadu a fagen zabe nan ba da jimawa ba, ina son tabbatar da cewa ni da shi 'yan uwan juna ne da kasarmu Najeriya ta haifa."

source@bbchausa

No comments:

Post a Comment