Thursday, February 07, 2019

ASUU called off strike

The leadership of the Academic Staff Union of Universities (ASUU) has suspended its nationwide industrial action.

National President of the union, Professor Biodun Ogunyemi, announced this on Thursday during a press briefing at the Nigeria Labour Congress complex in Abuja.
The striking lecturers took the decision after a meeting with representatives of the Federal Government led by the Minister of Labour and Employment, Senator Chris Ngige.
The meeting came hours before Professor Ogunyemi announced the decision of ASUU to suspend the strike.
It had in attendance leaders of the union and government representatives such as the permanent secretaries at the ministries of Education, as well as Labour and Employment, and some directors from the ministries

Friday, February 01, 2019

Ba za mu yarda da shishshigi ba – Buhari

Lauyoyin Alkalin Alkalai da aka dakatar Walter OnnoghenHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionLauyoyin Alkalin Alkalai da aka dakatar Walter Onnoghen
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta amince da abin da ta kira shishigin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidanta ba.
Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce "mun yi watsi da duk wani katsalandan ko kuma wani tunanin da ke son cusa tsoro ko rusa sahihanci da karbuwar tsarin zabenmu."
Gwamnatin Najeriyar ta ce za ta yi maraba da duk wani mai sha'war ganin an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya da kuma Amurka suka nuna damuwa game da dakatar da Alkalin Alkalan kasar, makwanni uku kacal kafin zaben Shugaban Kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda yake neman wani wa'adi, ya dakatar da Alkalin Alkalai Walter Onnoghen a ranar Juma'a game da zarge-zargen saba dokokin bayyana kadarori.
Babbar jam'iyya adawa ta Najeriya PDP ta bayyana matakin a matsayin wani kama-karya, sannan ta dakatar da yakin neman zabenta na wucin-gadi.
Dakatarwar ta janyo cece-kuce, saboda idan har aka kalubalanci sakamakon zaben shugaban Kasar, Alkalin Alkalan ne zai taka mahimmiyar rawa wajen yanke hukuncin wanda ya lashe zaben daga karshe.
Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka sun bayyana damuwa kan cire Alkalin Alkalan, suna masu cewa matakin zai iya zama matsala ga zaben kasar.
Tawagar masu sa ido ta tarayyar Turai a zaben Najeriya ta yi kira ga dukkanin bangarori na siyasa su bi tsarin doka da kundin tsarin mulki ya tanadar.
Amurka da Birtaniya sun nuna damuwa ne kan yadda aka dakatar da Alkalin alkalan ba tare da amincewar majalisa ba.
Birtaniya ta ce wannan zai iya cusa shakku a ciki da wajen kasar kan muradin gudanar da sahihin zabe a Najeriya.
Amurka ta ce yadda dakatar da Alkalin Alkalan ya janyo suka game da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma 'yancin bangaren shari'a, hakan na iya kawo cikas ga alkawalin da gwamnati da 'yan takara da jam'iyyun siyasa suka yi na tabbatar da ganin an yi sahihi kuma karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.
Amma a martanin da ta mayar, fadar shugaban Najeriya ta ce a shirye ta ke ta tabbatar an gudanar da sahihin zabe amma ba za ta amince da katsalandan daga waje ba kan harakokin da suka shafi cikin gidanta.
Alkalin Alkalai na riko Ibrahim Tanko MuhammadHakkin mallakar hotoADESHINA/FACEBOOK
Image captionAlkalin Alkalai na riko Ibrahim Tanko Muhammad
source@bbchausa.com

Mun yafe wa Buhari zuwa Zamfara — Marafa

Sanata Kabiru MarafaHakkin mallakar hotoORDER PAPER
Daya daga cikin masu neman takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a jam'iyyar APC, wanda bangarensa ba ya ga-maciji da gwamnatin jihar, sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce sun dauke wa shugaba Muhammadu Buhari zuwa jihar yakin neman zabe.
A cikin wata hira da ya yi da BBC, sanata Marafa, ya ce jihar Zamfara ta shugaba Buhari ce, kuma su mutanensa ne suna kuma tare da shi tsakani da Allah.
Amma bisa la'akari da abin da ke faruwa a jihar, sanata Marafa ya ce ' Ina son zan ba wa Baba shawara na cewa mun dauke masa zuwa jihar Zamfara, ya bari mu za muyi masa duk abin da ake yi, kuma kuri'unsa ba bu abin da zai taba su'.
Ya ci gaba da cewa 'Amma idan mai girma shugaban kasa ya ga cewa yana so ya je Zamfara, to za mu roke shi ya sawwake mana zuwa tarbarsa a ranar da zai zo, idan dai har gwamnatin jihar za ta tarbe shi'.
Sanata Marafa, ya ce, idan har shugaban kasar ya je jihar, to bayan ya tafi su za su hada masa gangami in ya so sai ya tura wakili ya gani, sannan kuma za su sa a haska gangamin a gidan talbijin na kasa NTA.
Wadannan kalamai na sanatan, sun zo ne bayan ikirarin da ya yi cewa suna da kwarin gwiwa za su shiga zabuka duk da matsayar hukumar zabe.
Hukumar zabe ta kasa dai ta sake jadada matsayarta cewa jam'iyyar ta APC ba ta da 'yan takara a jihar Zamfara saboda rikicin da ya faru a lokacin zabukan fidda gwani.
Jam'iyyar APC a jihar dai ta rabu gida biyu, wato akwai bangaren gwamnan jihar mai ci Abdul'aziz Yari da kuma daya bangaren.
Wannan layi ne
Rikicin siyasa a Zamfara dai ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.
Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.
Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.
Jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara bangaren gwamnan jihar, ta ce sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, a ranar Alhamis, ta mika wa hukumar zaben ta tarayya jerin sunayen 'yan takararta a zabukan da za a yi batun da hukumar zabe ta yi watsi da shi.
source@bbchausa.com

Wednesday, January 23, 2019

An kama masu shirin kai wa musulmai hari a Amurka

Vincent Vetromile, Brian Colaneri and Andrew CryselHakkin mallakar hotoGREECE POLICE DEPT
Image captionSunayen mutane hudun Andrew Crysel mai shekara 18, da Vincent Vetromile mai shekara 19, da kuma Brian Colaneri mai shekara 20.
An kama wasu mutum uku da wani yaro daya da ake tuhumarsu da hada baki don kai hari kan wata al'ummar musulmai a jihar New York.
Ana zargin mutanen ne da hada bama-bamai da bindigigogi da kuma shirin kai hari kan al'ummar Islamberg, wadda wani malami dan kasar Pakistan ya kirkira a shekarun 1980.
An gano shirin kai harin ne bayan da a wata makaranta wani dalibi ya jiyo tattaunawar da wasu dalibai 'yan uwansa ke yi na kitsa kai harin.
Al'ummar Islamberg ta zamo wani waje da ake yawan zargin ta zama kamar sansanin horar da masu tsattsauran ra'ayi.
Za a gurfanar da mutanen a gaban kotu ranar Laraba.
Sunayen mutane hudun Andrew Crysel mai shekara 18, da Vincent Vetromile mai shekara 19, da kuma Brian Colaneri mai shekara 20.
Dukkansu ana tuhumarsu da laifin mallakar makamai da shirya kai hari. Ana kuma tuhumar daya yaron mai shekara 16.
'Yan sanda sun ce a kalla uku daga cikinsu sun yi aiki a matsayin 'ya sikawut.
Masu bincike sun ce, kungiyar wacce take Birnin Greece da ke arewa maso yammacin jihar, ta samar da a kalla abubuwan fashewa ta hanyar amfani da manyan jarkoki da tulunan gas da allurai da sauran muggan abubuwa.
An same su a gidansu yaro mai shekara 16 din, a cewar 'yan sanda. An kuma samu bindigogi 23 a wasu wuraren daban-daban.
New York state map
Al'ummar Islamberg na zaune ne a yammacin tsaunukan Catskill kuds fs Birnin Binghamton.
Mafi yawan Amurkawa 'yan asalin Afirka suna zaune ne a wannan yanki don gujewa cunkoson da ke Birnin New York.
Mazauna yankin sun bayyana al'ummar a matsayin mai son zaman lafiya da kywaun mu'amala, sai dai wasu kafafen yada labarai na bayyana su da cewa sansanin hirar da masu tsattsauran addinin musulunci ne.
source@bbchausa.com

Tuesday, January 22, 2019

Muhawarar Jihar Kano: Kalubalen da ke jiran gwamnan Kano na gaba

kanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAna yi wa Kano kirari da jalla babbar Hausa
Kano ta Dabo tumbin giwa, tunjumin gari mai Dala da Gwauron Dutse, gari ba Kano ba dajin Allah! Wannan shi ne kirarin da aka jima ana yi wannan birni ko in ce jiha, wadda za a iya cewa kusan ita ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.
A yanzu dai a iya cewa kwanaki ne suka rage kafin ranar da za a yi zabukan Najeriya da suka hada da na gwamnoni a jihohin kasar, ciki kuwa har da Kano.
Haka kuma, a nan BBC muka zage wajen shirya muhawara ta 'yan takarar gwamna a wasu jihohin kasar da suka hada da Kanon, kuma aski ya zo gaban goshi, domin kuwa ranar 31 ga watan Janairun nan ne za a tafka ta tsakanin 'yan takara hudu maza da kuma mace daya.
kano durbarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Masu sharhi na ganin wannan muhawara tana iya sauya al'amura da dama, musamman sauya ra'ayin masu zabe kan wanda za su zaba, bayan sun ji shirin da kowane dan takara ke da shi.
A wannan makala dai, BBC ta yi nazari ne kan irin kalubalen da ke gaban duk wanda zai lashe zaben na 2019 na kujerar gwamnan Kano, da kuma nazari kan irin yadda zai iya tunkararsu.
Wannan layi ne

Matsalolin Jihar Kano

Hakika duk wanda ya san jihar Kano to ya san babbar jiha ce da ba za ta rasa wasu manyan matsaloli da ke damunta ba, duk kuwa da irin ci gaban da ake samu da kuma sauye-sauye da wasu gwamnatoci na da da na yanzu suka samar mata.
Sai dai ba za mu mayar da hankali kan dukkansu ba, za mu zabi muhimmai ne daga cikinsu, wadanda muke ganin su ne manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.

Cunkoson jama'a

cunkoso a KanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Masana harkokin yau da kullum da dama a jihar Kano sun bayyana cewa cunkoson jama'a da kara tutudowar mutane cikin jihar na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.
Malam Kabiru Sa'idu Sufi wani mai sharhi ne, kuma malami a makarantar share fagen shiga jam'ia ta Kano, ya shaida wa BBC cewa: "Yawan jama'ar da ke kara shiga Kano ya sa abubuwan more rayuwa ba su wadata ba.
"Babu isassun tituna, babu isassun makarantu, ruwan sha, wutar lantarki duk ba su ishi yawan al'ummar jihar ba," in ji Malam Sufi.
Sai dai ya ci gaba da cewa: "Duk wanda zai zama gwamna yana bukatar bayar da kulawa ta musamman kuuma ta gaggawa - don bukatar ta fi karfin abun da ke kasa a yanzu."

Bangaren ilimi

Malam Kabiru Sa'idu Sufi ya kara da cewa harkar ilimi a jihar Kaduna na ci gaba da tabarbarewa musamman a matakin.
Ilimi a jihar KanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
"Yawan haihuwa da cunkoso a makarantun jihar musamman ganin hotunan da suka dinga yawo a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan, sun isa shaida wa mutum cewa harkar ilimi na cikin halin ha'u'la'i.
"Don haka duk wanda zai zamo gwamna na gaba na bukatar sanya dokar ta baci don shawo kan lamarin.
"Akwai bukatar kara yawan malamai, da ba su horo da kara yawan makarantu da samar da dukkan kayayyakin aiki a ake bukata," in ji Malam Sufi.

Lafiya uwar jiki

Rashin isassun asibitoci da wadatattun kayan aiki da isassu kuma kwararrun likitoci da ma'aikatan jinya na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta, kamar yadda Malam Sufi ya ce.
Ya kara da cewa: "Don haka ya zama wajibi ga gwamna mai zuwa ya dauki matakan da suka dace don kai wa gaci."

Yankunan karkara

Noma tushen arziki in ji masu magana, kuma kamar yadda aka sani mafi yawan manoma mazauna yankunan karkara ne, don haka akwai bukatar samar musu da filin noma da iri da taki da kuma dabarun noman zamani, in ji masanin.

Tattalin arziki

Kamar yadda aka sani ne tattalin arzikin Najeriya ba ma na Kano ba na fuskantar babban kalubale, don haka Malam Sufi ke ganin akwai bukatar bai wa dama su samu kudade a hannunsu.
"Babu kudo a hannun manoma da 'yan kasuwa, kuma hakan babban kalubale ne ga ci gaban tattalin arziki.


Kano masana'antu
Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
"Akwai bukatar samar musu da hanyoyin samun kudi a kuma samar wa mata jari a horar da su kan sana'o'i," a cewar masanin.
Yanzu dai abun da za a jira a gani shi ne, yadda gwamnan da zai lashe wannan zabe mai zuwa zai tunkari wadannan kalubale tare da warware su don ci gaban jihar Kano.


dalar gyada
Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA da Kano na da arzikin gyada inda ake fitarwa wasu kasashen

Sunday, January 20, 2019

Mutum 30,000 aka raba da muhallansu a Barno- MDD

Kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a wasu yankunan jihar Barno a watan Janairun 2019Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a wasu yankunan jihar Barno a watan Janairun 2019
Majalisar Dinkin Duniya ta ce karuwar rikicin Boko Haram a cikin 'yan makwannin nan ya yi sanadiyar raba mutane fiye da dubu talatin da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.
Rundunar sojin Najeriya ta tsaurara kai hare-hare ta sama da ta kasa a kan mayakan na Boko Haram domin maida martani ga hare-haren da masu tayar da kayar bayan suka zafafa kai wa a baya-bayan nan.
Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta damu matuka game da halin da farar hula ke ciki.
A bangare guda kuma rundunar sojin Najeriya ta ce ga alama 'yan Boko Haram sun labe a wasu kauyuka a kewayen birnin Maiduguri inda suka saje da jama'ar gari, kamar yadda za ku ji a a wannan rahoto na.
Kimanin mutane 20,000 ne suka iso wani sansanin gudun hijira a cikin maiduguri da ya riga ya cunkushe bayan sun sha wahalar tafiya.
Mai kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Mr Edward Kallon ya ce ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira kuma ya tarar da su a cikin mawuyacin hali.
Ya ce suna kwana a waje, sannan suna matukar bukatar taimakon abinci daruwa da tsaftataccen wajen kwana.
Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da ke bukatar wurin kwana a Monguno ba.
source@bbchausa.com

MDD: 'Yan ci-rani 170 sun mutu a tekun Bahar Rum

More than 4,200 migrants reportedly crossed to Europe in the first 16 days of 2019Hakkin mallakar hotoEPA
Image captionKimanin 'yan gudun hijira 4,200 ne suka tsallaka teku zuwa Turai a kwanaki 16 na shekarar 2019 kawai
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 170 ne suka mutu a wasu hatsarin jirgin ruwa biyu da suka auku a tekun Bahar Rum.
A wata sanarwa da shalkwatar hukumar ta fitar a birnin Geneva, ta ce labarin mutuwar mutanen ya gigita ta, kuma ta yi kira ga kasashen Turai da su tashi tsaye wajen samar wa 'yan gudun hijira hanyoyi masu sauki na shiga nahiyar Turai.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce wani jirgi da ya dauko 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani akalla 50 ya nutse a yammacin tekun Bahar Rum tsakanin Maroko da kasar Spaniya.
Mutum daya ne kawai ya tsira da ransa, wanda shi ma wani jirgin masunta ne ya tsinto shi.
Wannan hatsarin ya biyo bayan wani irinsa da ya auku, inda sojojin ruwa na kasar Italiya na can na neman wasu mutum 117 da ba a san inda suka shiga ba, kuma mutum uku kawai aka gano kawo yanzu.

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta ce ba za ta iya tabbatar da yawan wadanda suka mutu ba, amma ya zama wajibi a kawo karshen wannan asarar rayukan da ake yi.
A migrant who was resued in the MeditaraneanHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionWani dan gudun hijira da aka ceto daga tekun Bahar Rum
Hukumar ta damu da matakan da wasu kasashen Turai ke dauka na hana kungiyoyin sa kai ceto irin mutanen da suka sami kansu a irin wannan mawuyacin halin.
A karshe hukumar na so a fitar da wani sahihin tsarin da zai hana 'yan gudun hijira shiga hannun masu fasa kwaurin mutane domin shigar da su Turai ta barauniyar hanya.
source@bbchausa.com