GETTY IMAGES
Fadar shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta yi watsi da maganganun da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan yayi cewa an sami karuwar cin hanci da rashawa a karkashin wannan gwamnatin idan aka kwatanta da lokacin da ya sauka daga mulki.
Sanarwar da kakakin Shugaban Najeriya Garba Shehu ya sanyawa hannu, ta karyata wannan hasashen da tsohon shugaban kasar ya wallafa a cikin wani sabon littafi da ya kaddamar a ranar Talata, inda gwamnati ta ce alkaluma ba sa karya idan aka duba zahirinabin da ke faruwa a kasar.
Sanarwar ta ce "Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihi a fannoni biyu. Na farko shi ne yadda gwamnatinsa ta tabbatar da bangaren shari'a na bin ka'idojin aikinsa, wanda ya hada da hukunta alkalai."
Sanarwar ta ce shugaban ne na farko da ya taba yin haka a tarihin kasar, inda ta kuma nuna cewa wannan ne karo na farko da aka gurfanar da manyan hafsoshin sojojin kasar a gaban kotu saboda zargi aikata laifukan da suka jibanci cin hanci da rashawa
Sannan kuma, wannan ne karon farko da jam'iyya mai mulkin kasar ta gurfanar da wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada da tsofaffin gwamnonin jihohi wadanda 'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne.
Kana wannan ne karon farko da kasashen duniya ke yaba wa Najeriya saboda nasarorin da ta ke samu a yakin cin hanci da rashawa, har ya kai ga an zabi shuigaba Buhari a matsayin zakara a cikin shugabannin nahiyar Afirka a fagen yaki da cin hanci da kuma rashawa.
JONATHAN TWITTER
Sanarwar ta lissafta wasu matakai da kudurin dokoki da kuma gyare-gyare ga wasu dokokin kasar domin inganta yakin da ta ke yi da masu cin haci da laifukan da ke gurgunta tattalin arzikin kasar:
Sanarwa ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da abin ta kira "bambamin da tsohon shugaban kasar ke yi a littafin nasa" inda ya ke ikirarin cewa shi ne ya samar da wasu shirye-shiryen da wannan gwamnatin ke tyunkaho da su kamar tsarin tantance ma'aikata, da tsarin nan na yi wa dukkan masu ajiya a banki rajista (BVN).
Saura sun hada da mayar da asusun ajiya na kasar ya zama guda daya tilo (TSA) da yadda aka hada bayanan albashin ma'aikatar kasar a wuri guda (IPPIS) domin yayi tunanin kafa tsare-tsaren ne amma ya kasa aiwatr da su.
A karshe sanarwar ta sanar da 'yan Najeriya cewa a lokacin da gwamnati mai ci ta karbi madafan iko a watan Mayun 2015, asusun ajiyar hukumar EFCC na da Naira biliyan 19.5 ne, kamar yadda wani rahoto na ofishin ministan shari'a ke dauke da bagyanan.
Kuma bayan shekara daya da fara aiwatar da yaki da "cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin ke yi, an sami karuwar kudade a cikin asusun zuwa Naira biliyan 279".
Source copied@bbchausa.com
No comments:
Post a Comment