@POLICENG
Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta ce ta samu amincewar kotu kan ci gaba da tsare Sanata Dino Melaye.
Wata sanarwa da ta fitar, rundunar 'yan sandan ta ce kotun tarayya a Abuja ta amince a ci gaba da tsare Dino Malaye har tsawon kwanaki 14 domin gudanar da bincike kan zarginsa da ake yana da hannu a yunkurin kisan dan sanda.
Sai dai ya musanta zargin.
'Yan sandan sun kuma ce ana kula da lafiyar Dino Melaye a wani asibitin gwamnati da ke hukumar tsaro ta cikin gida (DSS) sabanin wasu rahotanni da suka ce an tafi da shi wani wurin da ba a sani ba.
Sai dai kuma wasu hotuna da ke yawo a kafofin sadarwa na intanet sun nuna Dino Melaye kwance a harabar asibitin, inda rahotanni suka ce ya ki amincewa ya shiga.
'Yan sanda dai sun tare ne a kofar gidan Sanatan mai wakiltar Kogi kusan mako daya har sai da ya fito ya mika kansa a ranar 4 ga watan Janairu.
'Yan sandan suna zargin Dino Malaye ne da yunkurin kashe wani jami'in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 ga watan Yulin 2018.
Rundunar 'yan sandan ta ce kotu ta ba ta damar ta ci gaba da tsare Dino Melaye har sai ta kammala bincike kafin ta gabatar da shi a kotu domin fuskantar hukunci.
source@bbchausa.com
No comments:
Post a Comment