GETTY IMAGES
Kano ta Dabo tumbin giwa, tunjumin gari mai Dala da Gwauron Dutse, gari ba Kano ba dajin Allah! Wannan shi ne kirarin da aka jima ana yi wannan birni ko in ce jiha, wadda za a iya cewa kusan ita ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.
A yanzu dai a iya cewa kwanaki ne suka rage kafin ranar da za a yi zabukan Najeriya da suka hada da na gwamnoni a jihohin kasar, ciki kuwa har da Kano.
Haka kuma, a nan BBC muka zage wajen shirya muhawara ta 'yan takarar gwamna a wasu jihohin kasar da suka hada da Kanon, kuma aski ya zo gaban goshi, domin kuwa ranar 31 ga watan Janairun nan ne za a tafka ta tsakanin 'yan takara hudu maza da kuma mace daya.
GETTY IMAGES
Masu sharhi na ganin wannan muhawara tana iya sauya al'amura da dama, musamman sauya ra'ayin masu zabe kan wanda za su zaba, bayan sun ji shirin da kowane dan takara ke da shi.
A wannan makala dai, BBC ta yi nazari ne kan irin kalubalen da ke gaban duk wanda zai lashe zaben na 2019 na kujerar gwamnan Kano, da kuma nazari kan irin yadda zai iya tunkararsu.

Matsalolin Jihar Kano
Hakika duk wanda ya san jihar Kano to ya san babbar jiha ce da ba za ta rasa wasu manyan matsaloli da ke damunta ba, duk kuwa da irin ci gaban da ake samu da kuma sauye-sauye da wasu gwamnatoci na da da na yanzu suka samar mata.
Sai dai ba za mu mayar da hankali kan dukkansu ba, za mu zabi muhimmai ne daga cikinsu, wadanda muke ganin su ne manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.
Cunkoson jama'a
GETTY IMAGES
Masana harkokin yau da kullum da dama a jihar Kano sun bayyana cewa cunkoson jama'a da kara tutudowar mutane cikin jihar na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta.
Malam Kabiru Sa'idu Sufi wani mai sharhi ne, kuma malami a makarantar share fagen shiga jam'ia ta Kano, ya shaida wa BBC cewa: "Yawan jama'ar da ke kara shiga Kano ya sa abubuwan more rayuwa ba su wadata ba.
"Babu isassun tituna, babu isassun makarantu, ruwan sha, wutar lantarki duk ba su ishi yawan al'ummar jihar ba," in ji Malam Sufi.
Sai dai ya ci gaba da cewa: "Duk wanda zai zama gwamna yana bukatar bayar da kulawa ta musamman kuuma ta gaggawa - don bukatar ta fi karfin abun da ke kasa a yanzu."
Bangaren ilimi
Malam Kabiru Sa'idu Sufi ya kara da cewa harkar ilimi a jihar Kaduna na ci gaba da tabarbarewa musamman a matakin.
GETTY IMAGES
"Yawan haihuwa da cunkoso a makarantun jihar musamman ganin hotunan da suka dinga yawo a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan, sun isa shaida wa mutum cewa harkar ilimi na cikin halin ha'u'la'i.
"Don haka duk wanda zai zamo gwamna na gaba na bukatar sanya dokar ta baci don shawo kan lamarin.
"Akwai bukatar kara yawan malamai, da ba su horo da kara yawan makarantu da samar da dukkan kayayyakin aiki a ake bukata," in ji Malam Sufi.
Lafiya uwar jiki
Rashin isassun asibitoci da wadatattun kayan aiki da isassu kuma kwararrun likitoci da ma'aikatan jinya na daga cikin manyan kalubalen da gwamna mai zuwa zai fuskanta, kamar yadda Malam Sufi ya ce.
Ya kara da cewa: "Don haka ya zama wajibi ga gwamna mai zuwa ya dauki matakan da suka dace don kai wa gaci."
Yankunan karkara
Noma tushen arziki in ji masu magana, kuma kamar yadda aka sani mafi yawan manoma mazauna yankunan karkara ne, don haka akwai bukatar samar musu da filin noma da iri da taki da kuma dabarun noman zamani, in ji masanin.
Tattalin arziki
Kamar yadda aka sani ne tattalin arzikin Najeriya ba ma na Kano ba na fuskantar babban kalubale, don haka Malam Sufi ke ganin akwai bukatar bai wa dama su samu kudade a hannunsu.
"Babu kudo a hannun manoma da 'yan kasuwa, kuma hakan babban kalubale ne ga ci gaban tattalin arziki.

"Akwai bukatar samar musu da hanyoyin samun kudi a kuma samar wa mata jari a horar da su kan sana'o'i," a cewar masanin.
Yanzu dai abun da za a jira a gani shi ne, yadda gwamnan da zai lashe wannan zabe mai zuwa zai tunkari wadannan kalubale tare da warware su don ci gaban jihar Kano.

GETTY IMAGES
No comments:
Post a Comment