
Komai ya yi farko tabas zai yi karshe kamar yadda masu iya magana ke cewa.
Bayan fafatawar da 'yan takarar kujerar gwamna hudu na jihar Gombe suka yi a muhawarar da BBC ta shirya, mun yi nazari kan irin yadda al'amarin ya kasance.
Wannan ne dai karo na farko da aka shirya muhawara irin wannan ta 'yan takarar gwamna cikin harshen Hausa a Najeriya, kuma ta jihar Gombe ita ce ta biyu cikin ukun da kafar yada labarai ta BBC ta shirya gabanin zaben 2019.
Muhawarar, wacce aka yi a birnin na Buba Yero, na cike da abubuwa na kayatarwa da ban sha'awa da ba za a yi saurin manta su ba, wadanda suka faru a wajen.
Ga dai jerin abubuwa bakwai da watakila su ne manyan lokuta na muhawarar, wala Allah wadanda suka ja hankalin mutane, ko suka fizgi hankalin mai kallo da sauraro.

Batun samar da ruwan sha
An tabo batun samar da ruwan sha sau da dama a yayin gudanar da muharar, daga tambayar da mai gabatarwa ya yi wa dukkan 'yan takara zuwa inda masu sauraro ma suka sake nanata tambayar kan tanadin da masu fafatawar suka yi wa al'ummar jihar Gombe kan batun.
'Yan takara sun zuba bayanai inda kowa ya dage ya jero irin shirin da yake yi wa kauyuka da cikin birni.
An ji Sanata Bayero Nafada na jam'iyyar PDP na jero irin ayyukan da ya yi wa jihar a bangaren samar da ruwan sha a lokacin da yake mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar da kuma kujerar majalisar dattawa da yake kai a yanzu.
Shi ma Inuwa Yahaya na APC ya ce yana da matakin da ya tanada na dogo da gajeren zango don samar da ruwan sha.
Barista Abdul-Ghaniy Bello na PRP ya ce zai kafa kwamiti don duba matsalar, zai kuma samar da rijiyoyin burtsatse.
Yayin da Wali Modibbo na APGA ya sha alwashin jan ruwa ta hanyoyi da dama da mutane za su wadatu da ruwa a Gombe da kewaye.
Wannan batu ya ja hankalin mutane sosai a zauren muhawarar.

Mafi karancin albashi: Inuwa da Bayero
A jerin tambayoyin masu sauraro, an yi wa Inuwa Yahaya da Bayero Nafada tambayar tanadinsu kan biyan mafi karancin albashi.
Inuwa na APC ya ce hakika zai biya naira 30,000 mafi karancin albashi, yayin da shi ma Bayero na PDP ya ce tabbas haka ne gaba-gaba wajen tsarinsa.
A wannan gaba ce zauren ya rude da tafi da sowa, jin ta bakin wadannan 'yan takara biyu.

"Fyade? Subhanallahi!!!"
Lallai ga duk wanda ya bibiyar muhawarar nan da wuya idan zai manta wannan lokaci da dan takarar APGA Wali Modibbo ya yi wannan kalamai.
An tambaye shi ne ta yaya zai magance matsalar fyade da ake yi wa mata a jihar Gombe ida ya zama gwamna.
Sai ya kada baki cikin nuna matukar al'ajabi ya ce, "Fyade? Subhanalillahi". A daidai wannan lokaci ne illahirin zauren da kuma masu bibiyar lamarin a waje suka rude da sowa da tafi sosai, inda har sai da mai gabatarwa da mai jawabi suka yi shiru, don jama'a su saurara.

Binciken gwamnati mai ci: Inuwa
Wannan na daga cikin tambayoyin da aka yi wa kusan dukkan 'yan takara kuma ta fito ne daga bakin masu sauraro.
Amsar Inuwa Yahaya na APC ta janyo hankalin mutane sosai, inda ya ce lallai zai binciki gwamnati mai ci a yanzu idan har ya zama gwamna.
Ya kuma kara da cewa zai tsuke bakin aljihun gwamnati.

Tsayuwar soja
Wani abu da ya sa illahirin dakin taron ya sake rudewa da dariya a lokaci guda shi ne yayin da mai gabatarwa Ibrahim Isa ya sanar da tafiya hutun rabin lokaci, ya kuma bukaci 'yan takara suna iya zama don su dan numfasa, amma sai Wali Modibbo na APGA, wanda kuma shi ne mafi yawan shekaru a cikinsu, ya ci gaba da tsayuwarsa kawai, bayan da duk sauran suka zauna.
An yi ta tafi da sowa har zuwa lokacin da hutun ya kare.
Ba na goyon bayan Buhari - Nafada
Lallai daga cikin al'amura ko batutuwan da suka ja hankali a wannan muhawara ba za a manta da wata tambaya da daya daga cikin masu sauraro ya yi wa Sanata Bayero ba, kan cewa ''Ko da gaske ne yana goyon bayan Shugaba Buhari na APC ne?"
Amma sai dan takarar na PDP ya ce: ''Ni ba na goyon bayan Buhari, Atiku nake goyon baya."
Irin tafi dasowar da mutane suka yi zai tabbatar maka da cewa lallai amsar tasa ta dauki hankali.

''Kukkuru-kuru"
A lokacin da aka zo jawabin rufewa daga bakin 'yan takara, kowa ya yaba da yadda abin ya kasance ya kuma yi godiya.
Amma Wali Modibbo sai ya kada baki ya ce mutane su zabi APGA ranar zabe, inda har ya karkatar da kai ya yi carar zakara ''Kukkurukuru, gidan da ba zakara ba ladanin asuba," in ji shi.
Lallai a wannan gaba ba mahalarta taron ba kawai har da mai gabatarwa Ibrahim Isa sai da ya tuntsure da dariya."
Sai kuma ya yi kira ga jama'a da kada su yi haddasa gaba a tsakanin 'yan takara domin dukkansu suna da alaka ko dai ta jini ko kuma ta auratayya. "Mu 'yan uwan juna ne," in ji shi.

Cincirundon magoya baya a waje
Wani abu mafi jan hankali bayan 'yan takara sun fita shi ne yadda daruruwan mutane suka yi dafifi suna jiran fitowar su, ai kuwa da yin arba da su sai aka dinga ihu da kirari iri daban-daban na 'yan siyasa.
Wannan abu ya sa hankalin ragowar mutane na ciki da ma na waje har suka fito don shaida me ke faruwa.

Sharhi, Halima Umar Saleh daga Gombe
Lallai a iya cewa wannan muhawara ta Gombe ta kare amma ta bar abubuwa da yawa da za a dade ana sharhi a kansu.
Dukkan 'yan takara dai sun yi kokari sosai wajen amsa tambayoyin da aka yi musu tare da buga misalai.
Ga alama matsalar ruwan sha na daga cikin manya da suka addabi jihar, don dukkan 'yan takarar sun yi ta nanata irin tanadin da suka yi kan haka.
Sannan a batun inganta ilimi ma 'yan takarar sun baje-kolin irin shirin da suke da shi.
Mafi yawansu dai sun fi jaddada muhimmancin kula da malaman makaranta wadanda su ne ginshikan da idan aka ba su kulawa to za a samu bai wa dalibai ilimi mai kyau.
A bangaren shirin 'yan takara kan inganta noma da tsaro ma dukkan su sun yi rawar ganin wajen bayyana irin tsarin da suke da shi kan hakan.

Sai dai wani abu da na lura shi ne, dukkan 'yan takarar babu wanda a karan kansa ya dauko batun tallafawa mata da tanadin da ya yi musu, da kuma batun mutane masu nakasa da na matasa har sai da masu sauraro da kansu suka yi tambayoyi kan hakan.
Daga nan ne kuma sai 'yan takarar suka zage suka yi ta jero bayanai da tanade-tanaden da suka yi wa wadannan rukuni uku masu muhimmanci na al'umma.
Sannan ga dukkan alamu Wali Modibbo ya sa mutane sun daddara da irin yanayin maganganunsa.
Wani abu da na sake lura da shi shi ne yadda 'yan takarar APC da na PDP suka mamaye harkokin siyasar, ga alama siyasar ta Gombe za ta ja hankali sosai a lokacin zabe.
Na kuma lura da yadda wannan muhawara ta zama wata dama ta sanin sauran 'yan takara biyu na PRP da APGA, wadanda a yadda na ji mutane na magana kamar ba a ma sansu a jerin 'yan takara ba sosai.
Wani abu mafi kayatarwa da kafar BBC ta yi a wannan muhawara kuma shi ne yadda dokokinta na tabbatar da ba a ci zarafin kowa ba suka yi aiki.

Tsaron da aka samar a wajen shi ma wani abin a zo a yaba ne kwarai, ta yadda aka zuba 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya da jami'an tsaro na kamfani mai zaman kansa da kuma na cikin makarantar FCE inda aka yi taron.
Sannan an raba dan abin taba ka lashe da 'yan kyaututtuka na jaka da riga da littafi mai tambarin BBC, ko da a ce kowa dai bai samu ba, to lallai zan iya cewa kashi 99 cikin 100 sun samu.
Sai mu ce Allah Ya kai mu muhawarar jihar Kano lafiya.
source@bbchausa.com
No comments:
Post a Comment