Sunday, December 30, 2018

Wasu mata da ke son zama gwamna a jihar Kano

Matan da ke son zama gwamna a Kano
Image captionMatan da ke son zama gwamna a Kano
A wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, mata da yawa sun fito takarar gwamna a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Jihar dai na daya daga cikin manyan jihohin arewacin Najeriya, kuma jiha ce wacce ta yi kaurin suna wajen tatagurzar siyasa.
A tarihin jihar dai mace bata taba rike wani mukami na shugabanci ba a matakin gwamna.
Matan bakwai sun fito ne a jam'iyyu daban-daban, kuma kowacce na da manufofinta na musamman ga al'ummar Kano idan ta lashe zaben.
Fauziyya Kabir Tukur ta zauna da hudu daga cikin wadannan matan ga kuma karin bayani a kan su.
Safiyya Salisu Abdul
Image captionSafiyya Salisu Abdul 'yar takarar gwamna a jihar Kano karkashin jam'iyyar NUP

Safiyya Salisu Abdul

  • Jam'iyya: National Unity Party (NUP)
  • Shekaru: 40
  • Karamar Hukuma: Dala Ward, unguwar Yalwa
  • Manufarta: "Idan aka zabe ni a matsayin gwamna a jihar Kano, zan tabbatar da tsaro ga al'ummata kuma zan dauki kyakkyawan mataki wajen ganin jihata ta yi zarra."
Halima M Ahmad
Image captionHalima M Ahmad 'yar takarar gwamna a jihar Kano karkashin jam'iyyar AD

Halima M Ahmad

  • Jam'iyya: Alliance for Democracy (AD)
  • Shekaru: 55
  • Karamar Hukuma: Gwale
  • Manufarta: "Idan na samu nasarar zama gwamna a jihar kano, zan tabbatar da cewa na yi aiki tukuru wajen ganin cewa al'ummar jihar sun samu martaba a kasarmu."
Maimuna Muhammad
Image captionMaimuna Muhammad 'Yar takarar gwamna a jihar kano karkashin jam'iyyar UPP

Maimuna Muhammad

  • Jam'iyya: United Progressive Party (UPP)
  • Shekaru: 40
  • Karamar Hukuma: Kano Municipal, unguwar Indabawa
  • Manufarta: "Na yi aikin sa kai a asibitoci, kuma na ga halin da mutanenmu ke ciki. Don haka na dau niyyar kawo ci gaba mai yawa a fannin ilimi da lafiya da samarwa matasa ayyukan yi."
Matan da ke son zama gwamna a Kano
Image captionMatan da ke son zama gwamna a Kano
Sauran 'yan takarar sun hada da Fatima Danladi Musa ta jam'iyyar RPN (Restoration Party of Nigeria), da Rukayya M Abdullahi ta jam'iyyar DPC (Democratic Peoples Congress) da Umma Ibrahim Adhama ta jam'iyyar CAP (Change Advocacy Party) da Furera Ahmad ta jam'iyyar FDP (Fresh Democratic party) da kuma Amina Yusuf ta jam'iyyar NAC (National Action Congress).


source@bbchausa.com

No comments:

Post a Comment