Thursday, December 13, 2018

Gwamnati za ta aurar da mutum 3000 a Kano

Gwamnati za ta aurar da mutum 3000 a Kano
Za a aurar da mata da maza 3000 a Kano
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya, na shirin aurar da mutum dubu uku da suka hada da zawarawa, da samari da `yan mata.
Tuni dai gwamnatin ta kafa wani kwamitin da zai tantance su tare da daura musu aure.
A cewar gwamnatin, matasa da dama na bukatar aure, amma rashin sukuni ya hana su, don haka ne take tallafa musu.
Gwamnatin jihar Kanon ta bayyana cewa taimaka wa masu bukatar yin auren, wata hanya ce ta kyautatawa, tare da kare mutuncin al`umma, don haka babu asara a cikin dawainiyar da za ta yi face riba ga jama`a.
Sabanin tsarin da gwamnatin ke bi a baya inda takan zabi zawarawa da `yan mata tana aurarwa, a wannan karon an shigar da samari a cikin mutum 3000 da za a yi wa auren.
Alhaii Ali Baba a Gama Lafiya, shi ne mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin addini, kuma mataimakin shugaban kwamitin da zai tantance su tare da daura musu auren ya kuma shaida wa BBC cewa,' Zamu aurar da 'yan mata wadanda ba su taba aure ba, wadanda yawancinsu rashin gatane ya hana a aurar da su.'.
Ali Baba a Gama Lafiya ya ce, za a aurar da 'yan mata 1000 da zawarawa mata 500 da zawarawa maza 500 sai kuma samari 1000.
Ya ce kuma gwamnatinsu ce za ta dauki nauyin dukkan kayan daki da sadaki har ma da gara.

Wannan layi ne

Karin bayani

Wannan dai ne shi ne karo na biyu da gwamnatin Abdullahi Ganduje ke tallafawa wajen yi wa mabukata aure.
A bara ma ta taimaka wa amare da angwaye fiye da 1500.
Sai dai yayin da gwamnati ke wannan agaji, a bangare guda kuma ana kuka da yadda aure ke yawan mutuwa a jihar Kanon, lamarin da wasu ke dangantawa da auren gata, inda ake wanke amare ana kai wa gidan miji ba tare da angwayen sun yi dawainiya ba, kuma irin wannan cin bulus din, a cewar masana na daga cikin dalilan da ke sa wasu mazajen suna yi wa auren rikon wulakanci, sannan kuma yana mutuwa.
Kuma wannan ne ya tambayi Alhaji Ali Baba a Gama Lafiya ko bay a ganin cewa da irin wannan auren-gatan ake sare tushen auren?
Nan da wasu makwanni ma su zuwa ne ake sa ran za a kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren mutum 3000 a lokaci guda a jihar

source@bbchausa

No comments:

Post a Comment