Tuesday, December 25, 2018

An yi zanga-zangar damuwa da yawan kashe-kashe a Zamfara

Zanga zanga a Zamfara
An kafa dokar hana fita a karamar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara bayan kone-konen da aka yi a zanga-zangar nuna damuwa da yawan kashe mutane da ake yi a jihar.
Akalla mutum uku 'yan sanda suka ce an kashe, yayin da suka ce sun kama mutum 23 daga cikin masu zanga-zangar da suka kira ta "masu zaman banza."
Mutanen jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zangar domin nuna damuwa da yawaitar kisan rayuka da ake yi a sassan jihar.
Ana gudanar da zanga-zangar ne a karamar hukumar mulki ta Tsafe, da ke nisan kusan kilomita 50 da Gusau babban birnin jihar.
Rahotanni sun ce matasa da 'yan gudun hijira da suka kunshi mata da yara kanana sun toshe babbar hanyar da ke zuwa Gusau, tare da kone wasu gine-ginen gwamnati.
Mazauna garin na tsafe na bayyana damuwa ne kan yadda masu gudun hijira ke ci gaba da tururuwa a yankin, suna guduwa sakamakon hare-haren da ake zargi yan bindiga da barayin shanu ke kai wa.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sun gaji da halin ko-in-kula da hukumomi suke nunawa a kan rashin tsaro a jihar.
Shugaban karamar hukumar Tsafe Alhaji Abubakar Aliyu ya shaida wa BBC cewa, sama da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a kauyuka daban-daban cikin mako biyu.
A makon da ya gabata, an kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a kauyen Birnin Magaji, inda nan ne kauyen da minstan tsaro a Najeriya ya fito.
source@bbchausa.com

No comments:

Post a Comment