Monday, November 19, 2018

Wanne dan takara Rahama Sadau za ta zaba tsakanin Atiku da Buhari?

Masu bibiyarta sun bayar da amsoshi daban-daban, amma da alama amsar da ta fi burge jarumar ita ce wadda wani mai suna A.B Danbatta ya bayar.
"Kowanne mutum shi zai yanke hukunci kan shugaban kasar da zai zaba na gaba, babu wanda zai yanke maka wannan hukuncin sai kai da kanka. Amma ina bayar da shawara ga dukkan 'yan Najeriya su zabi mutum na gari ko daga wacce jam'iyya yake."
Daga nan ne Rahama Sadau ta nuna gamsuwar ta inda ta ce "Wannan ita ce amsar da nake so a ba ni πŸ‘πŸΏπŸ‘πŸΏ.Allah ya yi maka albarka πŸ™ŒπŸΏ
Ba kamar takwarorinta na Kannywood da suka fito fili suka bayyana dan takarar da za su goya wa baya ba, da alama dai jarumar ba ta da zabi a zaben 2019.
Tuni dai jarumai irinsu Adam A. Zango da Fati Shu'uma da makamantansu suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Sai dai jarumai irinsu Sani Danja da Fati Mohammed da Maryam Booth sauransu sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar za su zaba a 2019.
Masu sharhi na ganin jaruman Kannywood ka iya sauya akalar zaben 2019, wanda aka kaddamar da yakin neman zabensa ranar Lahadin da ta wuce.

Source@bbchausa.com

No comments:

Post a Comment